Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 16:18-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.

19. Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.

20. Dukan 'yan'uwa suna gaishe ku. Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba.

21. Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna.

22. Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!

23. Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku.

24. Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙauna, albarkar Almasihu Yesu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 16