Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 16:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi.

2. A kowace ranar farko ta mako, kowannenku ya riƙa tanada wani abu, yana ajiyewa gwargwadon samunsa, kada sai na zo tukuna, a tara gudunmawa.

3. Sa'ad da na iso, sai in aiki waɗanda kuka amince da su da wasiƙa, su kai taimakonku Urushalima.

4. In ya kyautu ni ma in tafi, to, sai su raka ni.

5. Zan zo gare ku bayan na zazzaga ƙasar Makidoniya, don kuwa ta Makidoniya zan bi.

6. Watakila zan jima a wurinku, ko ma in ci damina, don ku yi mini rakiya duk in da za ni.

7. Ba sona ne in gan ku a yanzu in wuce kawai ba, a'a, ina sa zuciya ma in yi kwanaki a wurinku, in Ubangiji ya yarda.

8. Amma zan dakata a Afisa har ranar Fentikos.

9. Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.

Karanta cikakken babi 1 Kor 16