Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:53-58 Littafi Mai Tsarki (HAU)

53. Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan.

54. Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa,“An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”

55. “Ke mutuwa, ina nasararki?Ke mutuwa, ina ƙarinki?”

56. Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari'a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi.

57. Godiya tā tabbata ga Allah wanda yake ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

58. Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15