Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:52-56 Littafi Mai Tsarki (HAU)

52. farat ɗaya da ƙyiftawar ido, da jin busar ƙaho na ƙarshe, domin za a busa ƙaho, za a kuma ta da matattu da halin rashin ruɓa, za a kuma sauya kamanninmu.

53. Domin lalle ne, marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan.

54. Sa'ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓar nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwar nan, a sa'an nan ne fa maganar nan da take a rubuce za a cika ta, cewa,“An shafe mutuwa da aka ci nasararta.”

55. “Ke mutuwa, ina nasararki?Ke mutuwa, ina ƙarinki?”

56. Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, Shari'a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15