Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:38-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Amma Allah yakan ba ta kama, yadda ya nufa, kowace ƙwaya da irin tata kama.

39. Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu.

40. Akwai halitta irin ta Sama, akwai kuma irin ta ƙasa. Amma ɗaukakar irin ta Sama dabam, ɗaukakar irin ta ƙasa kuma dabam.

41. Ɗaukakar rana dabam, ta wata dabam, ta taurari kuma dabam. Wani tauraro kuwa yakan bambanta da wani a wajen ɗaukaka.

42. Haka kuma yake ga tashin matattu. Akan shuka su da halin ruɓa, akan kuma ta da su da halin rashin ruɓa.

43. Akan shuka da wulakanci, akan tasa da ɗaukaka, akan shuka da rashin ƙarfi, akan tasa da ƙarfi.

44. Akan shuka da jikin mutuntaka, akan tasa da jiki na ruhu. Da yake akwai jiki na mutuntaka, lalle kuma akwai jiki na ruhu.

45. Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa.

46. Amma ba shi na Ruhun nan ne ya fara bayyana ba, na mutuntaka ne, daga baya kuma sai na Ruhu.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15