Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 15:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A yanzu kuma, 'yan'uwa, zan tuna muku da bisharar da na sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi,

2. wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.

3. Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,

4. cewa an binne shi, an ta da shi a rana ta uku, kamar yadda Littattafai suka faɗa,

5. ya kuma bayyana ga Kefas, sa'an nan ga sha biyun.

6. Sa'an nan ya bayyana ga 'yan'uwa fiye da ɗari biyar a lokaci guda, yawancinsu kuwa suna nan har zuwa yanzu, amma waɗansu sun yi barci.

7. Sa'an nan ya bayyana ga Yakubu, sa'an nan ga dukan manzanni.

8. Daga ƙarshen duka ya bayyana a gare ni, ni ma da nake kasasshe, marar cancanta.

Karanta cikakken babi 1 Kor 15