Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 14:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba.

2. Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun al'amura yake ambato ta wurin Ruhu.

3. Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin yă inganta su, ya ƙarfafa su, yă ta'azantar da su.

4. Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa.

5. To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.

6. To, 'yan'uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba?

Karanta cikakken babi 1 Kor 14