Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 13:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala'iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo.

2. Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.

3. Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.

4. Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura.

5. Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kārā, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo.

6. Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya.

7. Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.

8. Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai shafe.

9. Ai, hakika iliminmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne.

10. Sa'ad da kuwa cikakken ya zo, sai ɗan kiman nan yă shuɗe.

11. Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya.

12. Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.

13. To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.

Karanta cikakken babi 1 Kor 13