Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 12:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Gaɓoɓinmu masu kyan gani kuwa ba sai an yi musu kome ba. Amma Allah ya harhaɗa jiki, yana ba da mafificiyar martaba ga ƙasƙantacciyar gaɓa,

25. kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya.

26. Ta haka, in wata gaɓa ta ji ciwo, duk sai su ji ciwo tare, in kuwa an yabi wata, duk sai su yi farin ciki tare.

27. To, ku jikin Almasihu ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.

28. A cikin ikkilisiya, Allah ya sa waɗansu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin mu'ujizai, sai masu baiwar warkarwa, da mataimaka, da masu tafiyar da Ikkilisiya, da kuma masu magana da harsuna iri iri.

29. Shin, duka manzanni ne? Ko duka annabawa ne? Ko duk masu koyarwa ne? Su duka masu yin mu'ujizai ne?

30. Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da waɗansu harsuna? Ko kuwa duka ne suke fassara?

31. Sai dai ku himmantu ga neman mafafitan bayebaye.Har ma zan nuna muku wata hanya mafificiya nesa.

Karanta cikakken babi 1 Kor 12