Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Kor 10:19-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Me nake nufi ke nan? Abin da aka yanka wa gumakan ne ainihin wani abu, ko kuwa gunkin ne ainihin wani abu?

20. A'a! Na nuna ne kawai cewa abin da al'ummai suke yankawa, ga aljannu suke yanka wa, ba Allah ba. Ba na fa so ku zama abokan tarayya da aljannu.

21. Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.

22. Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

23. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.

24. Kada kowa ya nemi ya kyautata wa kansa, sai dai ya kyautata wa ɗan'uwansa.

25. Ku ci kowane irin abu da ake sayarwa a mahauta, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.

26. Don an rubuta, “Duniya ta Ubangiji ce, da duk abin da yake cikinta.”

27. In wani a cikin marasa ba da gaskiya ya kira ku cin abinci, kuka kuwa yarda ku tafi, sai ku ci duk irin da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya ba saboda lamiri.

28. In kuwa wani ya ce muku, “An yanka wannan saboda gunki ne fa,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan mai gaya muku, da kuma saboda lamiri,

Karanta cikakken babi 1 Kor 10