Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Amintaccen Mai Riƙon Amanar Alherin Allah

1. Tun da yake Almasihu ya sha wuya a jiki dominmu, sai ku ma ku ɗauki irin wannan ra'ayi. Ai, duk wanda ya sha wuya a jiki, ya daina aikata zunubi ke nan,

2. domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.

3. Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama.

4. Suna mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, kuna zarmewa, kuna aikata masha'a irin tasu, har suna zaginku.

5. Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari'a.

6. Shi ya sa aka yi bishara har ga matattu ma, waɗanda ko da yake an yi musu hukunci a cikin jiki kamar mutane, su samu su rayu a ruhu kamar Allah.

7. Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a.

8. Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.

9. Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba.

10. Duk baiwar da mutum ya samu, yă yi amfani da ita ga kyautata wa ɗan'uwansa, a kan amintaccen mai riƙon amanar alherin Allah iri iri ne.

11. Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Shan Wuyar Kirista

12. Ya ƙaunatattuna, kada ku yi mamakin matsananciyar wahalar da ta same ku a kan gwaji, kamar wani baƙon abu ne yake faruwa a gare ku.

13. Amma, muddin kuna tarayya da Almasihu a wajen shan wuyarsa, sai ku yi farin ciki, domin sa'ad da aka bayyana ɗaukakarsa, ku yi farin ciki da murna matuƙa.

14. Albarka ta tabbata a gare ku in ana zaginku saboda sunan Almasihu, don Ruhun ɗaukaka, wato Ruhun Allah yā tabbata a gare ku.

15. Sai dai kada shan wuyar ko ɗaya daga cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi.

16. Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna.

17. Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?

18. “In adali da ƙyar ya kuɓuta,Me zai auku ga marar bin Allah da mai zunubi?”

19. Saboda haka, sai duk masu shan wuya bisa ga nufin Allah su danƙa ransu ga Mahalicci mai aminci suna aikata abin da yake daidai.