Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 2:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ku barori, ku bi iyayen gidanku da matuƙar ladabi, ba sai na kirki da masu sanyin hali kaɗai ba, har ma da miskilai.

19. Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.

20. To, ina abin taƙama don kun yi haƙuri in kun sha dūka a kan laifin da kuka yi? Amma, in kun yi aiki nagari kuka sha wuya a kansa, kuka kuma haƙura, to shi ne abin karɓa ga Allah.

21. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku. Gama Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa.

22. Bai taɓa yin laifi ba faufau, ba a kuwa taɓa jin yaudara a bakinsa ba.

23. Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuma bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari'ar adalci.

Karanta cikakken babi 1 Bit 2