Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Bit 1:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.

14. Ku yi zaman 'ya'ya masu biyayya. Kada ku biye wa muguwar sha'awarku ta dā, ta lokacin jahilcinku.

15. Amma da yake wanda ya kira ku mai tsarki ne, ku ma kanku sai ku zama tsarkaka a cikin dukan al'amuranku.

16. Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”

17. Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.

18. Domin kun sani an fanshe ku ne daga al'adunku na banza da wofi da kuka gāda, ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa da zinariya ba,

19. sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo.

20. An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe.

21. To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

22. Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.

23. Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.

24. Domin“Duk ɗan adam kamar ciyawa yake,Duk darajarsa kamar furen ciyawa take,Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,

25. Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,”Ita ce maganar bishara da aka yi muku.

Karanta cikakken babi 1 Bit 1