Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 142:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina kira ga Ubangiji don neman taimako,Ina roƙonsa.

2. Na kawo masa dukan koke-kokena,Na faɗa masa dukan wahalaina.

3. Sa'ad da na yi niyyar fid da zuciya,Ya san abin da zan yi.A kan hanyar da zan biMaƙiyana sun kafa mini tarko a ɓoye.

4. Na duba kewaye da ni, sai na ga ba ni da wanda zai taimake ni,Ba wanda zai kiyaye ni,Ba kuwa wanda ya kula da ni.

5. Ya Ubangiji, na kawo kuka gare ka na neman taimako,Ya Ubangiji, kai ne mai kiyaye ni,Kai kaɗai nake so a rayuwata duka.

Karanta cikakken babi Zab 142