Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta 'ya'ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.