A safiyar rana ta huɗun, suka tashi tun da wuri, domin su yi shirin tafiya, amma mahaifin matar ya ce masa, “Ka dakata ka ƙara cin abinci tukuna sa'an nan ka tafi.”