'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo,Su rusuna, su nuna bangirma.Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki.Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’