Ubangiji ne ya halicci sammai,Shi ne wanda yake Allah!Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta,Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo!Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba,Amma wurin zaman mutane.Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji,Ba kuwa wani Allah, sai ni.