Suna ce wa mutanen Yahuza, “Ku faɗa mana abin da za mu yi. Ku kāre mu, ku bar mu mu huta a inuwarku mai sanyi kamar inuwar itace da tsakar rana. Mu 'yan gudun hijira ne, ku ɓoye mu inda ba wanda zai gan mu.