Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka bisa ƙasar Masar domin fara ta zo. Farar kuwa za ta rufe ƙasar Masar, ta cinye duk tsire-tsire da ganyayen da suke cikin ƙasar, da iyakar abin da ƙanƙara ta rage.”