Ga mahaifinsa kuwa ya aika da jakai goma ɗauke da kyawawan abubuwa na Masar, da jakai mata goma ɗauke da tsaba, da kuma abinci da guzurin hanya saboda mahaifinsa.