Sai Yeshuwa ɗan Yehozadak tare da 'yan'uwansa, firistoci, da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel tare da 'yan'uwansu, suka tashi suka gina bagaden Allah na Isra'ila domin a miƙa hadayu na ƙonawa kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, mutumin Allah.