Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?