Amma na ji ka iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya bayyana mini ma'anarsa, to, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin mulkin ƙasar.”