1. Jama'ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.
2. Yehowahaz yana da shekara ashirin da uku sa'ad da ya ci sarauta, ya kuwa yi mulki a Urushalima wata uku.
3. Sai Sarkin Masar ya tuɓe shi daga sarautarsa ta Urushalima, ya sa su biya gandu, su ba da azurfa talanti ɗari, da zinariya talanti guda.
4. Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan'uwansa, sarki a Yahuza da Urushalima. Ya sa masa sabon suna Yehoyakim. Amma Neko ya ɗauko Yehowahaz ɗan'uwan Eliyakim ya kai shi Masar.
5. Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara goma sha ɗaya yana sarauta a Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnsa.