Yosiya kuwa ya kawar da dukan abubuwan banƙyama daga dukan ƙasar da jama'ar Isra'ila suke da ita. Ya sa dukan waɗanda suke a Isra'ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. A dukan kwanakin ransa, ba su kauce daga bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.