Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa'ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama suka ce, “Shi jikan Yehoshafat ne wanda ya nemi Ubangiji da zuciya ɗaya.”Don haka a gidan Ahaziya ba wanda ya isa ya riƙe mulkin.