Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.