6. Waɗannan kuma su ne 'ya'yan Ehud, maza. Su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu da suke zaune a Geba, waɗanda aka kai su bauta a Manahat.
7. Ga sunayensu, Na'aman, da Ahaija, da Gera wanda yake shugabansu lokacin da aka kai su bauta. Shi ne kuma mahaifin Uzza da Ahihud.
8. Shaharayim kuma yana da 'ya'ya maza a ƙasar Mowab bayan da ya saki matansa biyu, wato Hushim da Ba'ara.
9. Matarsa Hodesh ta haifa masa 'ya'ya maza, su ne Yobab, da Zibiya, da Mesha, da Malkam,