A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.