Sa'ad da Isra'ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra'ila sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.