Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko'ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi.